3 Satumba 2020 - 10:46
Gwamnati Da “Yan Tawayen Sudan Sun Gana Da juna Domin Fara Aiki Da Yarjejeniyar Sulhu

Kamfanin dillancin labarun Sudan na ( SUNA) ya nakalto cewa; A jiya Talata an yi ganawar ne a tsakanin kwamandojin gamayyar kungiyoyin ‘yan tawaye ta ( SRF) da kuma gwmanatin rikon kwarya inda su ka tattauna hanyoyin aiki da yarjejeniyar sulhun da su ka cimmawa a tsakaninsu.

ABNA24 : Shugaban gamayyar kungiyar ‘yan tawaye ta Sudan Alhaji Idris ya bayyana cewa; “Wannan shi ne lokacin farko da aka yi ganawa a tsakanin bangarorin biyu tun bayan rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhun.”

Shi kuwa shugaban kungiyar ‘yan tawaye ta yankin Darfur Minni Minawi ya bayyana cewa; Muhimman abubuwan da suke gabanmu su ne bunkasa tattalin arziki da ayyukan jin kai ga mutanen da suke a daidaice.

Gamayyar kungiyar ‘yan tawayen ta Sudan ta kunshi mayakan yankunan Darfur, da Kurdufan ta kudu da arewa da kuma Blue Nile.

342/